Yadda Zuku Duba Sakamako Karo na Biyu na Daukar Ma’aikatan IMMIGRATION

Yadda Zuku Duba Sakamako Karo na Biyu na Daukar Ma’aikatan IMMIGRATION

Hukumar Shige da Fice ta Najeriya ta ce takusa kammala shirye-shiryen tantance sunayen ‘yan takara domin ci gaba da daukar ma’aikata na shekarar 2023.

Hukumar a cikin wata sanarwa a ranar Juma’a ta bayyana cewa tana kan kammala tattara sunayen ‘yan takarar da za a tantance a fadin Jihohin kasar nan, inda ta kara da cewa an samu nasarar tantance jerin sunayen jahohi da na shiyya, kuma nan da wani lokaci hukumar za ta fitar da sanar wa a hukumance. 

Hukumar ta Shige da fice ta Nageria ta kuma bayyana cewa,bayan tantance ‘yan takara na daukar ma’aikata na shige da fice na shekarar 2023, ‘yan takarar za su gudanar da gwajin Kwamfuta (CBT), domin kuma tana kammala shirye-shirye tare da Cibiyoyin ICT da CBT a shirye-shiryen fitar dakuma sunayen wadanda su tantance.

Ana sa ran duk masu neman wannan takara da ake kira ‘yan takara su lura cewa ya zuwa yau “Za a ci gaba da daukar ma’aikata duk da jinkirin da aka samu na fara ayyuka da tsarin da suka fara da jerin sunayen da ake jira.

“Gaba dayan jerin sunayen suna kan ci gaba kuma kusan an kammala su, an yi nasarar tantance jerin sunayen jahohi da na shiyya-shiyya kuma nan da wani lokaci hukumar za ta buga wa jama’a a hukumance.

“Hukumar ta karyata gaba daya yadda ake yada sakonnin gayyata ga gwaje-gwajen CBT da suka hada da Tax Clearance don haka ta ba da shawarar cewa ‘yan takara su daina su yi watsi da irin wadannan bayanan  banata bane.

Check Also:  Labari Mai Dadi, an Sake Bude Shafin Daukar Ma'aikata a Shafin eHealth4everyonee

A yanzu hukumar ta fara shirye-shirye Buɗe yanar gizonta a Hukumance Domin duba jerin sunayen wadanda suka yi Nasarar shiga fagen Farko Jerin sunayen da CBT za su biyo baya, 

Zaku iya dubawa anan: https://cdcfib.career/

in ji Hukumar Shige da fice ta Nageria

www.haskenews.com.ng

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *