Aiki a Hukumar INEC: INEC Ta Bude Shafin Daukar Ma’aikatan Zabe (Adhoc Staff) a Jahohi uku (3) da Za’ayi Zabe Kwanannan

A ranar 11 ga watan Nuwamba ne ake sa ran za a gudanar da zaben a jihohin Bayelsa da Imo da kuma Kogi. Hakan yasa hukumar INEC ta bude shafin cike aiki da yakunshi supervisory presiding officers, presiding officers, assistant presiding officers, registration area technicians, and registration area centre managers. 

  • Zaben Gwamna a Jahohin Bayelsa, Kogi da Imo na 2023
  • Ranar rufe aikace-aikacen shine “Oct 2, 2023

Abubuwanda ake bukata a wajan cikewa 

  • 1. Adireshin imel mai aiki. 
  • 2. Lambar wayar hannu mai aiki. 
  • 3. Lambar asusun banki. 
  • 4. Hoton fasfo na kwanan nan (farin bango, ƙarƙashin 5MB). 
  • 5. Referees guda biyu tareda adireshin imel da lambar wayarsu. 
  • 6. Tabbataccen ID na ma’aikaci ko ID na ɗalibi (kamar yadda aka nuna akan katin ID ɗin ku). 
  • 7. Lambar Kammala NYSC ga tsofaffin yan bautar kasa (ba kafin 2018 ba). 
  • 8. NYSC Callup Number ga wadanda keyiwa kasa hidima yanzu (2022). 
  • 9. Kwafin kwalin karatu a tsarin PDF. 
  • 10. Kwafi na ID card a tsarin JPG ko JPEG.

Yadda zuku cike 

Domin cike aikin zabe na wucan gadi ku latsa shafin yanar gizo da ke a kasa

Shafin Cikewa: https://pres.inecnigeria.org/app/inec-iasd/applicant/registration

Allah yasa mu dace baki daya

www.haskenews.com.ng

Check Also:  Daukar aiki: Hukumar Immigration Service zata gudanar da Physical Screening/Certificate Verification exercise

Leave a Comment