Rundunan yan sanda najeriya zata dauki sababin ma’aikata za’a bude yanar gizon nema daukar ma’aikatan 15 ga watan October 2023

Ku tabbatar kun cike dukkan ka’idojin da rundunan yan sanda ta gindaya domin samun nasarar cin gajiyar shiga aikin. 

Dalilai barkatai da suke hana mutanan mu samun duk wani abu da gwamnatin tarayya data bude, rashin karanta sharudan dake cikin yanar gizon hukumar.

Wurin neman aikin ko cike wani abu daban da gwamnatin tarayya ta bude ba’a bukatar mutum yayi gagawa abu a hankali wurin cikewa, ka tabbata abun da suka tambaya kasa a wurin kada ka sanya musu abun da basu bukata ba. 

Karanta ka’idojin yana da mutukar mahimmanci ga mai nema domin ta nan ne kadai zaka iya gano abubuwan daya dace ya nema dasu,dole mu bi a hankali mu natsu wurin karanta bayanai da hausa ko da turanci duk abun daka gani ba kayi tambaya ga wanda suka iya karatun turanci yafi dacewa ma kaje cafe idan har ka tabbata sun iya aiki zaka iya zuwa wurin su. 

Shawara ga masu nema aikin ko wani abu daban. 👇

Ku sane wani bawa bai isa ya baku abun da Allah bai kaddara ba, kada kace ka dade kana nema baka samu ba ka cigaba da nema ka sanyawa zuciyarka cewa Allah ne kadai zai kaddara ka samu ko rashin samun. 

komai lokaci ne a wannan rayuwar da kuke gani idan lokacin samun aikin ka baiyi ba wallahi tallahi ko shugaban kasa ne ya haifi ka ba zaka samu ba, idan ko lokacin samun aikin ka yayi zaka raina kaddarar silar samun aikin ka. 

Komai zamuyi mu nemi shawarar iyaye don su sanya mu acikin addo’in su Allah ka cigaba da ciyar damu alheri. 

Check Also:  Masu Kwalin SSCE, OND, NCE, HND, BSc, MSc da Ph.D an Bude Shafin Daukar Ma'aikata a eHealth4everyone

Ga masu sha’awa sai su yi rijista ta wannan hanyar yanar gizo www.apply.policerecuitment.gov.ng 

Ayi share don sauran alumma su amfana suma Allah ya bamu nasara

www.haskenews.com.ng

Leave a Comment