YADDA AKE ZAMAN AURE – Haskenews-All About Arewa

Biyaiya ga miji, dolene amtsayinki na matar aure dolene kiyi biyaiya acikin duk abinda mijinki yace kiyi inhar be sabawa abinda Allah da manzon shi sukace ba, kiji aranki kefa bautar Allah kika zoyi, kuma kisa aranki cewa aure hanyace da zaki nemi  aljanna da ita. Fadin gaskiya, fadin gaskiya akoda yaushe kowana lokaci  yanada mahimmanci kuma ze  jawo miki kauna da soyaiyar mai gidanki, kuma ze jawo miki yadda Allah da monzon shi,Rikon Amana, ki kasance mai rikon amanar mijinki ki kiyaye kanki daga duk wani na miji wanda ze iyasa mijinki ya zargeki akansa, ki yanke alaka ga duk Wanda mijinki baya so kiyi alaka dashi, ki kula da dukiyarshi da duk abin amfani ma gida ko kuma kadararshi ko kuma kudinshi, kada ki sake ki zama me duba aljihun mijinki wai don ki samu kudi aciki Sam wannan ba daidai bane idan kikaci kinci haram matukar ba baki yaiba kuma duk sanda Yakama kimarki zata rago awajanshi ki kiyaye. Dole ne ki zamo me kunya, dolene ta guji duk abinda zesa mijinta yaji kunya agaban jama a  ta kiyaye

Ki zamo me hakuri,kada kiyi tunanin Rabin ranki baze bata maki raiba, wasu mutanen idonsu yana rufewa  wai don it a  kadaice ya mace agidansu ko itace yar auta ko ita kadai aka Haifa agidansu kada kiyi tunanin yadda ake shagwaba ki agidanku kice ai dole ma agidan mijinki haka za ai miki koda yaushe zaki iya samun miji kamar haka amma dole wataran asaba akan haka, to kada kiji haushi koki fusata, kiyi hakuri kiyi kokarin mantawa da komai daya faru idan ya faru, Wanan ze kara miki zaman lafiya agidanki mijinki. Iya magana ki zamanto mai iya magana ga mijinki kada kiyi tunanin aina kinzo gidan yanci kema kinada dama fadar kowaca magana, ba haka bane mijinki dole shine agaba koda ace kin girmeshi ko kuma kuna Sa a dashi ko kuma yabaki shekara kadan, zena ganin kin rainashine, saboda yana ganin cewa shine gaba kuma shine mai gida kuma akowana lokaci yana ganin yanada ikon da zeyi abinda yaga dama agidanshi, kada yana baki labari mai mahimmanci kice, to “tsaya ka rantse” ! Wanan zesa yaga kin raina mishi hankali harya fara tsanarki. Ki tsaya ki nutsu alokacin dayake fada miki wani abu mai mahimmaci, kada yana magana kicigaba da abinda kikeyi, idan yai magana kada kice inajinka ba kunnene yake jiba ko kice ni ka dameni, gaskiya hakan ze iya jawo miki matsala babba, kuma ze iya canza yanayin ma amalarshi dake, ke kuma hakan ze iya hanaki kwanciyar hankali agidan mijinki. Ki kasance mai godiya aduk lokacin da mijinki yayi miki wani Abu komai kankantarshi yin hakan yanada mahimmanci kuma yana karo soyaiya atsakanin ma aurata haka zalika godiya ga mijinki zesa akara miki Wanan abunma da bakiyi tunaniba, idan yai miki wani Abu kika gode seya samu kwarin gwiwar yi miki wani abu, amma idan baki godeba ko kika raina abinda ya kawo miki, to nan gaba ko yayi tunanin yi miki wata kyauta seya fasa saboda yana tunanin karya kawo miki ki wataa mashi kasa a ido

Check Also:  Yadda zaku cike sabon tallafin NITDA Coursera scholarship cohort 2

Neman shawara miji kafin ki aiwatar da Abu nada kyau, Neman shawarar maigidanki  idan zakiyi wani abu zesa yaji ashe kin  daukeshi da muhimmanci kuma zeyi kokarin ya baki shawara daidai gwargwado, kada ki kasance mai yawan mita duk abinda akai miki kice se kinyi magana, ko maigidanne yai miki laifi ko wani daga danginshi, hakan yanada illa sosai ga rayuwar zaman aurenki, domin yana daya daga dalilan da mata sukafi yawa awuta alahira kamar yadda yazo a hadisi Annab( s a w ) yaan cewa lokacin dayai sallar idi seyaiwa mata huduba, yace kuwayaiwa sadaka saboda kune makamashin wuta ran lahira,  saboda kun kasance kuna yawan kai kara, kuma kuna yawan butulcema mazajenku, wadannan abubu biyu zasu iya kai mutum wuta, ki kasance  mai yawai godiya ga miji kuma kada ki yawaita magana akan wani Abu da bekai ya kawoba. Ki kasance mai temakon miji idan kina dashi acikin gida, ki ragemai wasu sha ani na cikin gida, zaki iya yiwa mijinki dinki be saniba sedai kawai yaga ankawo kaya adinke, ko kidau nauyin wani Abu agida, kibada kudi ayi idan dukiyar takima tanada yawa sosai zaki iya idan zaki zakka kuna kinsan mijinki ya cancanta zaki iya fitarwa ki bashi. Ki zamo mai kyawun alaka ga sauran mutanen dasuka shafi mijinki, wadannan sun hada da iyayen miji, abokiyar zama, yayyun miji da kannenshi, ya yan miji da bake kika haifaba, Yayan da kika haifa, abokanna arziki ya zama dole ki kula da wandanan mutanen gaba daya, kuma ki mutunta  kowa acikinsu.

www.haskenews.com.ng

Leave a Comment