Zabukan Kano Daga 1998-2019 Kashi Na Karshe

ZABUKAN KANO: DAGA 1998 -2019

Kashi na karshe

Daga wannan dan takaitaccen tarihi zamu gane cewa soja sun yi zabe biyu da shekarar 1998 da 1999. Shekarau ya yi zabe na kananan hukumomi sau biyu. An yi zabukan cike gurbi sau uku a zamaninsa. Daga 1999 har zuwa 2011 Kwankwaso bai yi zabe ba, amma da shi da tsaginsa na PDP sun shiga zabuka a Kano a wadannan shekaru har kashi takwas, babu inda suka samu nasara cikakkiya.

Haka kuma daga wadannan bayanan, zamu fahimci gwamnati mai ci a kowane lokaci tana amfani da karfin mulki, ma’ana tana amfani kudi da hukumominta don kaiwa ga nasararta. A kokarin haka kuma ana iya rasa rai ko dukiya ko mummunan rauni jama’a. A duk zabukan da aka yi na cike gurbi babu inda jam’iyya mai mulki ta yi asara. Babu wani rahoto na kalmomin tunzuri da tada hankali da rashin mutunci ko a rediyo ko a jarida ko akan duro a birni ko a karkara da Shekarau ya ke amfani da su a tsawon mulkinsa a tarukan siyasa. A tsawon wadannan shekaru gwamnatin ANPP tana kiyaye wa wajen bin umarnin kotu a sabgar da ta shafi zabe. A guri uku kotu ta kwace kujerar ANPP, an bi ka’ida an maida su ga ahalinsu. Wanda ya fara cin wannan gajiyar shi ne Alhaji Falalu Umar ciyaman na Ungoggo da Hon Ali Haruna Makoda, wanda a halin yanzu kwamishina ne.

Mu koma baya. Bayan an yi dukkan zabuka na gwamna da ciyamomi, a shekarar 2007 gwamnati ta zauna da gindinta ta ci gaba da mulki. A gefe guda ita kuma jam’iyyar PDP ta samar da shugabanci a shekarar 2010 karkashin jagorancin Barista Faruk Iya Sambo, wannan shugabancin bai karbu ba a gun Marigayi Abubakar Rimi da wasu masu binsa, ganin haka sai Kwankwaso ya tsara yawon yi wa jama’ar da suka zabi mutanensa kan mukami godiya da ban gajiya. A shekarar 2010 ne aka fara amfani da kalmar Kwankwasiyya, wacce sojan baka Mustapha Jarfa ya kirkirota. Duk Asabat da Lahadi na kowane sati Kwankwaso yana zuwa Kano gabatar da wannan taro. Abin ya samu tagomashi kuma sai ya zama kamar wani salon kamfen ga PDP. Ko sau daya Shekarau bai hana ‘yan Kwankwasiya wannan taruka ba. Sai da aka yi wata shida cur ba fashi aka zagaya 44LG. Sannan aka kara uku na sanatoriya uku ta Kano, an yi a Bichi da Rano da Gezawa. Taruka 35 dani aka yi su.

Check Also:  Zabukan Kano 1998 - 2019 Kashi na 2

A wannan yawon ne Kwankwaso ya kawo sabon fasalin kamfen. Duk fita ana tara matasa da muggan makamai, kuma kowane sati a wuraren tarukan nan akan bude kasuwar kayan maye a fili. Duk wani nau’in kayan maye zaka same shi freely ana sayarwa.

Idan kuma an hau mumbari za a yi jawabi, ba a fadar alheri sai kalilan, jamhuru da bariki da shegantaka yafi yawa, masu zuwanma sun fi sonsa.Ana karfafawa matasa su yi rashin kunya da rashin mutunci. Ana tsorata masu mulki. Misali, a Tofa Alhaji Sani Abdullahi Tofa ya gargadi Shekarau cewa ko 2011 a basu mulki ko a mutu. A Gwale ABDULLAHI Abbas ya fada Sabon Sarki, Sabon Gwamna. A Dambatta da Fage da Madobi da Dala Kwankwaso ya kira matasa su tanadi makamin kurada da jan tadi da Shelltox da kayan aiki da ‘yar sanda ta Fulani. Ali Baba da Ganduje a Kura da Fage sun fadi kazaman kalmomi.

Daga wannan lokaci har zuwa zaben 2011 matasa suka shiga tawagar Kwankwaso, kuma suna daukarsa gwarzo, jarumi da zai yi maganin masu ci da addini da suka zo suka lalata lamura. A cikin gida ANPP tana da

da nata matsalolin, matasa kuma suna son su dana mulki su sakata su sharbi romon democracy.

A wajen fitar da ‘yan takarar PDP da aka yi tsammanin za a samu rigima ko sabani, Kwankwaso ya yi dabara, ya dauke hannunsa ya bari wanda jama’a suke so suka kai labari ta hanyar bin ka’idar jam’iyya, musamman tunda zai tsira da tasa kujerar ta takarar gwamna. A son ransa Ghali Na Abba ya yi takarar senate Kano Central, dole ya hakura Lado ya yi nasara, wannan misali daya ne kawai. Ita kuma ANPP sai ta yi amfani da karfin gwamnati ta dora wanda take so.

Check Also:  Tarihi : Zabukan Kano 1998- Zuwa-2019 Kashi Na 1

Wannan salon kamfen da Kwankwaso ya yi amfani da shi a kakar zabukan 2011shi ne irinsa na farko a wannan jamhuriya a jihar Kano. Watakila ya yi haka ne, domin ya rama rashin mutuncin da ya ke zargin an yi masa a Kano.

An yi mummuna zabe a 2011, a zaben farko, na shugaban kasa, an salwantar da rayuka da dukiyoyi maras adadi. Da zabe na biyu ya zo, an yi bata-kashi, na kuri’a, kowane dan takara a tsakanin Kwankwaso da Takai sai da ya samu kuri’a miliyan daya da doriya. ANPP ta hakura ta barwa PDP nasarar da ta samu, bayan an kai gwauro da mari akan sakamakon mazabar Dala LG. Amma ANPP ta shigar da kara wacce aka yi wata shida ana bugawa, daga karshe aka barwa Kwankwaso nasararsa.

Da ya hau kan kujerar gwamna. Kwankwaso ya yi zabe guda biyu. Ya fara da zaben cike gurbi a Gaya da Garko a 2013. Kafin zaben an yi yakin kamfen a dimokuradiyyance a tsakanin PDP da ANPP, duk da an samu tashin hankula. A takaice ma dai yawon kamfen na karshe da Shekarau ya shirya yi fasawa aka yi, saboda tanadin tsiya da aka shirya daga bangaren gwamnati.

A ranar zaben kuwa na Garko da Gaya a 2013 sabon samfuri da Kwankwaso ya zo da shi ne, gayyato duk ‘yan jam’iyya na sauran kananan hukumomi da mafarauta da ‘yan sara da suka suka hallara a wajen zabe tun tsakiyar dare. Sun kwana a wajen zabe suka hana kowa ya yi zabe, sai wanda suka tanada don aikin dangwale. Haka a yi zaben suka fadi sakamakon yadda suka tsara. An yi wannan a Kano, ya wuce, yanzu sai tashin zancen. Attahiru Jega ya yi babatunsa ya gama babu abin da ya faru har zuwa yau. Kwankwaso ya dawo gida aka rika zuwa yi masa murna.

Check Also:  Microsoft OneNote: Save and sync your notes with all your devices

Haka aka sake yin irin wannan samfurin zaben a kananan hukumomi. Kazar Kwankwaso ta kyankyashe kwai 44 babu bara-gurbi ko daya. APC ta Kwankwaso ta zama tana da ciyamomi 44 da kansiloli 484. Ya fada da kansa cewa ramuwa ya yi da daukar fansa.

Wannan mumnar sunna ita Ganduje ya kwaikwaya a zaben cike gurbi na Minjibir wanda aka yi a shekarar 2016. Na sa ma ya fi na baya muni, wanda Awwalu Ubale dan takarar majalisa na PDP ya shiga rediyo ya ce ya janye takararsa don kada a zub da jini. A zaben kananan hukumomi ma da Ganduje ya shirya a karshen 2017 da farkon 2018 haka aka yi wannan tsarin. Jin dadin wannan samfurin ne ma Ganduje ya yi alkawarin zai baiwa Buhari kuri’a miliyan biyar in zaben 2019 yazo na shugaban kasa.

Maimaici aka yi na yadda aka yi zaben Garko da Gaya da Minjibir wadanda INEC ta kasa ke shirya wa a zagaye na biyu na zaben gwamna a Kano a 2019.

Rubutawa Bello Muhammad Sharada

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *