Zabukan Kano 1998 – 2019 Kashi na 2

ZABUKAN KANO:DAGA 1998-2019

Kashi Na Biyu

Zaben gwamna na 2007 ya bar baya da kura. Ba a samu biyan bukata ba. Haka PDP ta yi Allah Ya ISA ta hakura. Amma duk wani agaji da gwamnatin tarayya zata bayar domin a karbe Kano daga hannun jam’iyyar ANPP to ta bayar da shi ta sigar jami’an tsaro da ma’aikatan INEC. An yi dabaru very sophisticated kuma widely amma ba a samu yadda ake so ba.

Yadda aka gudanar da wannan zaben ya kara wa Kwankwaso da mabiyansa karfin gwiwa. Ya basu haske da jin kanshin sake dawowa kan gwamnati. Don haka suka kara damara don tunkarar zaben kananan hukumomi da suke sa rai za a yi ba jimawa. Ciyamomin da suke mulki a zamanin Shekarau, wasunsu tun shekarar 2003 suke kantomomi, daga nan suka zama ciyamomi zababbu, suka sake zama kantomomi, sannan kuma sune suke son takara a karo na hudu. A wannan yanayin kuma ga ajandar mataimakin gwamna Abdullahi Gwarzo da tasu Abdullahi Sani Rogo akan wanda zai nemi gwamna a 2011. A cikin gida wasu na so a buda su shiga, sun ga yadda ake warwasawa a LG, daga waje kuma akwai hamayya mai karfi.

Da aka zo wajen fidda ‘yan takara na ciyamomi bata sauya zani ba. Su din dai su aka baiwa. Ita kuma PDP da AC suka fito da sabbin ‘yan takara kar, masu farin jini, kusan ko ina a Kano. Mallam Shekarau a wurare daban-dabam ya yi alkawarin zai bada dama a yi zabe na LG sahihi, wanda ya ci a ba shi. Ya maimaita cewa zai tabbatar da adalci sau barkatai. Wannan alwashin bai gamsar da ciyamomi ba da suke cikin daular mulki da mataimakin gwamna da yake kallon lokacinsa ya yi kusa ya zo.

Check Also:  Tarihi : Zabukan Kano 1998- Zuwa-2019 Kashi Na 1

A wannan yanayi aka sa zabe a watan Nuwamba 2007. An yi zabe sahihi, lafiya-lafiya.Magana ta gaskiya an bari kowa ya zabi abin da yake so kuma cikin lumana. Amma da sakamako ya fara fita, sai ya nuna alamun PDP ce zata cinye duka guraren. Ga shi gwamna Shekarau baya Najeriya yana Saudiyya ya tafi hutu, ya bar mataimaki shi ne wuka da nama.

A lissafin mutanen siyasa na ANPP in suka bayar da nasarar zaben LG ga PDP to a ganinsu ANPP ta fadi zaben 2011 wanda yake tafe a shekaru hudu masu zuwa. Don haka a cikin daki aka shirya hana masu nasara, nasararsu. A cikin LG guda 44 an baiwa kananan hukumomi uku na PDP zabensu, a cikin birni akwai Kumbotso, amma a Kano Central, sai aka tsakura musu kansiloli, irinsu Yaya Kwaya na Yakasai. Oscar na Nassarawa yana da ransa ku tambaye shi tsakaninsa da Nasiru Gawuna.

Zafin wannan mataki ya harzuka ‘yan PDP, nan da nan kananan hukumomi suka kama da wuta. An kona Gwale da Minjibir da Wudil da Tofa da akalla sakatariyoyi goma. Gurin da zabe bai yiwu ba, aka yi musu kantomomi. An yi haka a LG shida kamar Garun Mallam. Irin kalaman da Kwankwaso da Ganduje suka yi kafin wannan zaben, yana cikin abubuwan da suka hassala kone-kone. Da kansa Ganduje ya je hukumar zabe ta jiha a Sabo Bakin Zuwo Rd, ya hau kan mumbari ya fadi munanan kalmomi akan Shekarau da gwamnatinsa, haka shima Kwankwaso, har sai da dan majalisar jiha na Gwale Umar Mathmetical ya yi kokawa da shi a filin Allah. Da Dr Abbati Bako da Barista Wada Bashir zasu iya bada shaida, suna nan da ransu.

Check Also:  Zabukan Kano Daga 1998-2019 Kashi Na Karshe

Gaskiya wannan zaben yana cikin abin da ya kara hura wutar gaba tsakanin tsagin Kwankwaso da Shekarau da masu binsu. Su mutanen RMK sun dauke shi wannan zaben a fashi da zalunci, wanda suka kudure a gaba zasu dauki fansa. Ita kuma ANPP ta dauke shi a matsayin ta’addanci da cin kashin ‘yan PDP ga gwamnati wanda ba zasu kyale ba.

Kafin wannan kurar kuwa da shekara guda, sai aka wurgo dan majalisar jiha na Nassarwa Sani Babankowa daga kujerarsa. Aka shirya zabe na cike gurbi a 2006, su Alhaji Yahaya Bagobiri da Bala Gwagwarwa daga PDP sun yi duk shirinsu, gwamnati ta shirya nata.

Kafin a kai ga samun mai rinjaye sai da aka yi ‘Inconclusive’. Zagaye biyu aka yi kafin a kawo karshe a wannan zaben. Kowa sai da ya taro danginsa da karfinsa. Karshe dai dan takarar gwamnati ya kai. Ku lura sosai a duk zabukan da aka yi ana barin masu hakki su yi zabe kuma ana yin zaben cikin gida ko sulhu ko baka ce da shi sahihi ba, zaka ce dama-dama, sannan a zabukan ba a fito da makamai tsirara a filin zabe, kuma wani ba ya yi wa wani zabe. Ba shakka baki suna zuwa a matsayin kowa ejan ko kowa security ko kowa canvasser in dai an zo cike gurbi ko karashen zabe.

Rubutawa Bello Muhammad Sharada

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *