Tarihi : Zabukan Kano 1998- Zuwa-2019 Kashi Na 1

Tarihi : Zabukan Kano 1998- Zuwa-2019 Kashi Na 1

BARI na fara da shimfida.Dimokuradiyya ita ce hanyar da muka zaba a wannan kasar tamu a matsayin tafarkin da za a rika amfani da shi don samar da shugabanni da zasu rika juya al’amuran rayuwar al’umma a zango zango.

Tsarin dimokuradiyya shi ne mulkin farar hula na siyasa. An dora shi akan ginshikin sahihin zabe da ‘yancin dan adam da baiwa kowa dama da kuma bin ka’ida.

Tarihi : Zabukan Kano 1998- Zuwa-2019 Kashi Na 1

ZABUKAN KANO: 1998- ZUWA-2019

Da yawa yadda ake gudanar da abubuwa a sauran sassan duniya, idan ka zo a Najeriya sai ka ga ba haka bane. Hatta wani lokacin ba kawai da Turawa da Larabawa muke sabawa ba, har da bakake ‘yan uwanmu ‘yan Afirka. Zaka ga abin kirki a kasar Ghana da South Africa, a Najeriya kuma abin banza.

Don haka a sauran sassan duniya, siyasa bautar al’umma ce da hidimtawa kasa, mu anan ita ce babbar hanyar samun kudi, kuma neman mulki shi ne mafi tsadar sana’a, ita ce kuma hanyar da kowa ya dauka ta marasa mutunci da aka fi asarar rayuka da dukiya.

Shekararmu 20 cif a wannan jamhuriyar ta hudu. An yi zagayen zabe har sau shida a duk fadin kasar nan. Zan maida hankali ne akan jihar Kano musamman saboda yadda zaben gwamna ya zo a 2019.

Zabukan farko gwamnatin soja ce ta Abdusalami Abubakar ta shirya su. Ta shirya na kananan hukumomi a 1998, sannan na shugaban kasa a 1999.

Tsaffin ‘yan siyasar jamhuriya ta farko da ta biyu da ta uku a Kano sune suka ci karensu ba babbaka. Suka rabu gida biyu wasu a APP, wasu a PDP. Wanda soja suke so sune suka samu nasara, a dayan biyun jam’iyyun. An kare zabukan babu wani tashin hankali mai yawa. A gaskiya a wannan lokacin jama’ar gari siyasar bata shiga jikinsu ba. ‘Yan siyasar na gidi, sune suka rika coge a junansu.

Tarihin Siyasar kano, kwankwaso, shekarau, Ganduje

Kwankwaso shi ya fara gwamnan siyasa a wannan jamhuriyya a Kano. Ya yi mulki drin salonsa da zabe ya zo Allah bai kaddara komawarsa ba, ya fadi. A zamansa na farko 1999 2003, bai gudanar da zabe ba ko na cike gurbi ko sabo fil na kananan hukumomi.

A shekarar 2004, ‘yan watanni da hawan Shekarau ya shirya zaben kananan hukumomi. Akasarin wanda suka yi wa jam’iyyar gwamnati ta ANPP takara sun rike kantomomi, ita kuma PDP tsaffin zababbu ne.

A lokacin, gwamnati tana sabuwa kuma ta saki linzami kowa ya zabi abin da ya yi masa. PDP ta samu ciyamomi hudu da suka hada da Makoda da Shanono da Rimin Gado da Garko duk da kotu ta juya wasu, sannan sun hada da samun kansiloli 76 cikin 484. Wannan ya karfafi PDP matuka.

A wannan shekarar dan majalisar Ajingi ya rasu, INEC ta kasa ta shirya zaben cike gurbi. ANPP ta tsayar da Kansila Hon. Abdul’aziz Gafasa. Daga wannan zaben aka fara yin fitar dango don yin reinforcement. Duk wani hamshaki a PDP daga kan Marigayi Abubakar Rimi har zuwa Baba Musa Gwadabe har kanana-kanana sai da suka halarci Ajingi da jama’arsu. Ita ma gwamnati ta shirya nata, an yi zabe an gama lafiya, ba a hana kowa Participation ba. ANPP tayi nasara.

An sake samun irin wannan zaben na cike gurbi a Makoda amma wannan karon a karkashin ofishin Ahmadu Haruna Zago sai aka shirya reinforcement. Da kuma aka je, sai da aka yi bata-kashi har da rasa ran dan adam da jikkata da dama. Wannan shi ne mafarin kisa. Ba zaka iya cewa ga mai tsokana ba, ga mai gaskiya ba. Haka ran ke salwanta ba a bin hakki, balle hukunci.

Tun saukar Kwankwaso daga gwamna da abubuwan da suka biyo baya na tuhumarsa da saka masa White Paper, sun saka ya samu sabani da Shekarau, wannan sabanin ya zarce a tsakaninsu da magoya bayansu. Hakan ya janyo ba komai a junansu sai zambo da habaici da gugar zana da kallon-kallo. Aka shiga derby shigen irin na Madrid da Barca ko Arsenal Da Man U, amma na siyasa.

A wannan sabanin, Kwankwaso sai da ya dauki cikakkiyar shekara biyar baya shiga sabgar Kano kai tsaye, sai dai daga Kaduna ko Abuja. Magoya bayansa kuma suna cike da damuwar kuntatawa ta siyasa. A gefe guda kuma ana fuskantar zaben kananan hukumomi bayan wa’adin na kai ya cika ga kuma zaben kasa baki daya.

An yi zaben gwamna mai zafi tsakanin ANPP da PDP. PDP ta tsayar da Kwankwaso da farko daga baya ta zare sunansa ta saka Ahmed Garba Bichi. Shi kuma suka kara da Mallam Shekarau. A wajen fadar sakamako da Nasiru Aliko Koki da Rabi’u Sulaiman Bichi a matsayinsu na wakilan PDP ficewa suka yi daga dakin da zargin an yi amfani da gwamnati an danne su. An yi tirka-tirka akan zaben Tudun Wada da Doguwa wanda basu gamsu da shi ba. Su kuma.wakilan ANPP su Garba Yusuf da Dokta Bashir Galadanci sun yi jayayya basu gamsu da na Bichi ba. A Bichi ANPP ta samu dubu 17 PDP kuma ta samu dubu 84 in ka hada jumlar abin da suka samu har da na AC da sauran jam’iyyu kuri’ar tafi yawan gaba dayan kuri’ar da aka baiwa mutanen Bichi daga INEC.

Ala dole ANPP ta hakura aka hada wa PDP wannan lissafi. Ita ma ANPP aka bar mata na Tudun Wada.

Rubutawa Bello Muhammad Sharada

Related

Stay on op - Ge the daily news in your inbox