SIFFOFIN WANDA AKE SO A AURA.
Akwai siffofi da ake so, miji da mata su kasance sun siffantu da su, tun kafin sunemi junansu da aure, don samar da farin ciki da natsuwa a tsakaninsu, ga su nankamar haka:-
(1) SIFFOFIN NAMIJIN DA ZA A AURA:-a.Ya zama mai addini, mai kiyaye dokokin Allah, ko da kuwa ba malami ba ne, donmai addini shi ne ake tsammanin kiyaye hakkokin auratayya daga gare shi.
(b.Ya kasance ya dan haddace wadansu Ayoyin Alqur’ani, don sukan kara wa bawaImani, wanda ya haddace ayoyin kuma yana kiyaye dokokinsu babban mutum ne awurin Allah.
(c.Ya zama mai tausayin mata, ba mai duka, zagi, takuri da cin mutunci ba, a indababu gaira babu dalili.
(d.Ya kasance yana da kuzarin biyan bukatan Iyalinsa da nemo mata abinci, suturi,wurin zama da abubuwan masarufi na yau da kullum tun da Annabi (SAW) yc”WANDA YAKE DA HALI DAGA CIKINKU YA YI AURE…” [Bukhaqi 5065, Muslim1400].
(e.Wanda ganinsa zai faranta ran matarsa, da samun zamantakewa mai kyau.
(f.Ya kasance ana tsammanin samun zuriya daga gare shi, akan gane hakanne tahanyar ‘yan uwansa ko zuriyars. Ko da yake haihuwa ta Allah ce, yana bayar da itaga wanda ya so, kuma yadda ya so, wani kuma sai ya sanya shi AQIM, kamar yaddayc”YA KAN SANYA WANDA YA GA DAMA AQIM (wanda ba ya haihuwa)” [Shura50].
(g.Kuma ya kasance ya dace da matar, ta wajen hali, matsayi da fahimtan juna, donsamun zaman lafiya. Anan nake jan hankalin ‘yan uwa mata da kada su kuskura suauri mutumin banza, mai halin mutanen iska, don za su shiga mayuwacin halin da zaisa ba za su ji dadin rayuwarta ba har abada! Duba (Sahih Fiqhis Sunnah 3/103-107).