Babban Bankin Najeriya (CBN) Ya Soke Lasisin Bankunan Kasuwanci 132

Dalilan da su ka fusata CBN soke lasisin Ƙananan Bankunan Kasuwanci 132

Ashafa MurnaibyAshafa Murnai  May 24, 2023

Dalilan da su ka fusata CBN soke lasisin Ƙananan Bankunan Kasuwanci 132

Babban Bankin Najeriya (CBN), ya fito da sanarwar soke lasisin wasu ƙananan bankunan kasuwanci 132 a faɗin ƙasar nan.

Bankunan waɗanda aka fi sani da game-garin suna ‘micro finance banks’, an soke su ne a cikin wata sanarwar da bankin ya fito da ita a ranar Talata.

CBN ya ce dukkan su sun kasa cika sharuɗɗa da ƙa’idojin da aka kafa masu a ƙarƙashin Dokar Kafa Ƙananan Bankunan Kasuwanci ta 12, BOFIA 2020, Mai Lamba 5.

Bankunan dai kamar yadda sanarwar CBN ta bayyana, an daina yin hada-hadar kuɗaɗe a cikin su a faɗin ƙasar nan, kuma sun daina kowace irin mu’amala da CBN, a matsayin sa na Babban Banki mai kula da dukkan cibiyoyin hada-hadar kuɗaɗe a ƙasar nan.

Haka kuma CBN ya ce an ƙara bai wa bankunan damar saisaita al’amuran hada-hadar su har tsawon watanni shida, amma ba su yi amfani da damar ba, kuma ba su cika sharuɗɗan ba, ballanata ɗorewar hada-hadar da ya kamata su ci gaba da yi.

Bayan su kuma an soke lasisin wasu bankunan bayar da jingina ko lamunin kuɗaɗe guda huɗu.

Sunayen Ƙananan Bankunan Kasuwanci 132 Da CBN Ya Soke Wa Lasisi:

1. Atlas Microfinance Bank

2. Blue whales Microfinance Bank

3. Everest Microfinance Bank

4. Igangan Microfinance Bank

5. Mainsail Microfinance Bank

6. Merit Microfinance Bank

7. Minna Microfinance Bank

8. Musharaka Microfinance Bank

9. Nopov Microfinance Bank

Check Also:  Rundunan yan sanda najeriya zata dauki sababin ma'aikata za'a bude yanar gizon nema daukar ma'aikatan 15 ga watan October 2023

10. Ohon Microfinance Bank

11. Premium Microfinance Bank

12. Royal Microfinance Bank

13. Statesman Microfinance Bank

14. Suisse Microfinance Bank

15. Vibrant Microfinance Bank

16. Virtue Microfinance Bank

17. Zamare Microfinance Bank

18. North Capital Microfinance Bank

19. Chidera Microfinance Bank

20. Excellent Microfinance Bank

21. Ni’ima Microfinanc

www.haskenews.com.ng

Leave a Comment