Yadda Zamu Tsara Curriculum Vitae (C.V) Domin Cike Aikin Gwamnati, Scholarships, NGOs Ko Tallafi

Curriculum Vitae (C.V) na daya daga cikin manyan matsalolinda ke janyo rashin samun aiki a duk lokacinda muka cike musamman aikin Gwamnati Scholarships, Tallafi ko NGOs haka yasa muka tsara samfura tare da bayanai dalla-dalla domin kacewa wannan matsalar. 

Kayi ta Applying din aiki ko Scholarship sau goma (10) ko sau ashirin (30) Sannan ko daya baka taba samu bah.

Wallahi Bawai ko baka da Sa’a Bane. 

Kuma ba wai an fika iyawa baneh.

Kawai Rashin Sanin cewa CV da COVER LETTER sune abu mafi mahimmanci Da Masu daukan aiki suka fi maida hankali akai, musamman ma aikin NGO.

Dayawa wayan ake dauka aiki ko bawa Scholarship zaka samu kafisu experience, grades da komai, amma sai karasa ya akayi Suka samu  kai baka samu bah. (Tabbas Allah neh mai bayarwa amma akwai Competency da kuma effort agun neman komai ) 

To sirrin shine Sun maida hankalin su Kan tsara CV da Cover later dinsu ta yadda zai dauki hankalin Company/Makaranta har su gayyace su Interview.

Aduk sanda Company/Makaranta ta gayyace ka interview, to INSHA’ALLAH aiki/Karatu yasamu, saidai idan sananin Rashin Rabo neh ya tabbata.

MENENE CV/RESUME

CV wadda yake nufin Curriculum vitae, document ne da yake nuna makarantun da kayi, work experience naka, skills naka da kuma irin abubuwanda kake so. A wasu kasashen ana kirashi da resume. 

TSAYIN CV?

Tsayin CV ya danganta da yawan experience naka da kuma kalan CV da zaka rubuta, amma mafi kyau kar CV ka ya wuce feji uku. 


ABUNDA CV YA KUNSA. 

Work experience 

Education

Contact details

Skills and achievements 

Language

Hobbies

References


GYARA CV  

A CV ka kafara da rubuta sunanka a matsayin title, ma’ana karkayi anfani da “Curriculum vitae” a title na CV. 

Saman title na CV ka ya zamto ka rubuta da 14 ko 16 font, kuma kayisa in bold. 

Check Also:  Masu Kwalin BSc, HND, NCE, OND Ko SSCE an Bude Shafin Cike Aikin Enumerator a "Anchor for Life Support and Resilience"

Ka zaɓi font kamar Calibri ko kuma Times New Roman a matsayin font naka. Girman font naka kayi anfani da 12 yadda masu daukan aiki zasu iya karantawa.

Kayi anfani da size iri ɗaya a duka rubutun da zakayi a CV. Ya zamu ka tsara CV ka daga karatu mafi kusa zuwa karshe, haka ma aiki. 

Kayi anfani da bullet points in zakayi list saboda zai kara kyaun CV. 

Idan ka gama rubutawa kayi saving da sunan ka, misali: “Mohammed Bukar CV” 

Kayi saving in PDF kafin ka tura CV ka. Amma akwai masu ɗaukan aiki da suke rubuta yadda sukeso, wasu na nema in Doc. 


ABUNDA ZAKA RUBUTA A CV

 

Kayi anfani da kalmomin da zasu nuna karfin abunda kake dashi. Misali: Professional, Proficient, exceptional da sauran su

CV mai kyau baya ɗauke da wata grammar ko spelling mistakes. Ka karanta CV ka mai kyau ka gyara duk wani spelling ko grammar error. 

Ka rubuta CV ka ya tafi da irin aikin da zaka cika. CV yana banbanta, misali teaching Cv, graduate trainee cv da sauran su. 

CV ka zai iya zama academic cv, chronological ko skills-based CV, ya danganta da irin aikin da zaka cika.

 Ya zamto email naka kayi anfani da sunanka ba wani abun daban ba. Misali mbmohammed@gmail.com yafi ace na rubuta mbguy@gmail.com 🤓. 

Ka guji yin karya a CV ka ko kuma saka abunda baka dashi a matsayin kana dashi. Misali: saka experience da baka dashi, matakin karatu, ko kuma jihar da kafito da sauran su. 


IRE-IREN CV


Cv ya rabu kashi kashi, akwai Academic Cv, Skill-based Cv da kuma Chronological Cv.


Chronological Cv wadda akafi sani da traditional Cv, Cv ne da ake lissafu aikin da akayi daga baya zuwa wadda akeyi. Ana jero aikin ne daga mafi kusa zuwa mafi nesa

Check Also:  Matsayar Shirin NSIP - Haskenews-All About Arewa

Academic Cv: Shi wannan CV ne da malaman Jami’a da na makarantun gaba da Secondary sukafi anfani dashi. 

Skill-based Cv: Shi wannan Cv ne na wanda yake da skills amma bashi da working experience ko kuma yanada karancin work experience. Misali graphic designer. 


Misalin Chronological Cv

Misalin Academic Cv

Misalin Skill-based Cv


MISALIN CHRONOLOGICAL CV.


1. Wannan shine misalin yadda zaka rubuta heading na CV ka:


               Mb Mohammed 

  Opposite ABC, Adjacent to XXX, LGA, Your State.  +23480000000                  example@gmail.com


Ya zamto ka fara da sunanka, address naka, number waya da email da za’a iya neman ka.

2. Yadda Zaka rubuta PROFILE SUMMARY


PROFILE SUMMARY


A resourceful humanitarian worker with wide experience in humanitarian activities in vulnerable communities in relief and development programs, strong knowledge of standard evaluative procedures and monitoring techniques, strong ability to address difficult problems through established approaches and techniques, proficient with data collection through simple or random sampling approach. A Proficient manager with ability to take leadership responsibilities with exceptional inter-personal, cultural and diplomatic skill.


3. Yadda zaka rubuta working experience naka:


WORKING EXPERIENCE


ORGANISATION: ABC International, XY LGA, XYZ STATE 

POSITION: Field Enumerator Jan 2019 – Date 

RESPONSIBILITIES:

Constant contact with local leaders to trace sampled households.

Organizing data in the field

Educating respondents on purpose of the survey and what it intends to achieve.

Any other task assigned by the supervisor.

Getting feedback from children through focus group discussion. 


working experience naka ka fara daga mafi kusa zuwa mafi nesa.


4. Matakin Karatu


Education

University of Maiduguri – B.SC Economics (Upper division) 2018


Wannan shine misalin yadda zaka jero makarantun da mayi. Ba dole bane sa grade da ka gama dashi.

5. Skills naka


 Skills


ODK Coding

Check Also:  SPO, PO, APOI, APOII, APOIII: Amsar Jarabawa da Hukumar INEC Zatayi Ayau

Excellent data entry skills (for both accuracy and speed)

Proven computer literacy in Microsoft office package such as (Microsoft word, excel & power point presentation).

Ability to operate office equipment and machines such as printer, scanner, photocopier machine etc.

6. Wannan bangare ne na certificates da kayi


Certifications


Certificate in Human Resources – Name na certificate issuer 

Certificate in Data Quality – 

Certificate in Data for Management use – 

Certificate in Safeguarding –

Certificate in Child protection in emergency setting

Certificate in Advance excel

Certificate in Computer science

Certificates naka kasa iya wadda suke da alaka da aikin da zaka cika, ma’ana ba duka zakasa ba in suna da yawa. Misali inada certificates sunfi hamsin, ba duka nake sawa akan CV ba. Idan kana bukatar samun certificates ka duba cousera, EDX, Udemy da sauran su. Zanyi rubutu a gaba yadda ake samun certificates kyauta musamman a wadda suke son aiki da international NGOs da companies.


7. PERSONAL INFORMATION


Sex : Male

Nationality : Country 

State of Origin : Your State

Local Government Area: Your Local government 

Marital status : Single

8. Language Spoken


English

Fulani

Hausa

9. Referees


Referees

Name: Misbahu Bichi 

Position: Database officer, ABC Company , Location State

Email: email of the referee

Phone number: phone number of the referee


Name: Mb Mohammed 

Position: Director, XYZ Company, Location of the organization

Email: email of the referee

Phone number: phone number of the referee


Name: Name of the third referee 

Position: M & E Officer, EDC Organization, Local government area, State Email: email of the referee

Phone number: phone number of the referee


Shi wannan bangaren zaka iya rubuta referees on request. Ma’ana in sunason referees zasu tambaye ka. Bashi da anfani sosai a sa shi. 


Idan kanada wata tambaya akan CV/Resume, ka ajiye tambayar ka a comment section. 

www.haskenews.com.ng

Leave a Comment