Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya kafa kwamitin shugaban ƙasa da zai binciki ayyukan hukumar NSIP mai kula da shirye-shiryen rage raɗaɗi a ƙasar.
Cikin wata sanarwar da mai magana da yawun shugaban ƙasar Ajuri Ngelale ya fitar, ya ce an kafa kwamitin ne domin maido da martabar shirye-shiryen da ya fara zubewa a faɗin ƙasar.
Matakin na zuwa ne bayan da a ranar juma’a shugaba Tinubu ya sanar da dakatar da shirye-shiryen rage raÉ—aÉ—in talauci huÉ—u da gwamnati ke aiwatar wa a Æ™asar na tsawon makonni shida.
Shirye-shiryen rage raÉ—adin da dakatarwar ta shafa sun haÉ—ar da shirin N-Power da, tallafin kuÉ—i ga marasa Æ™arfi, da shirin tallafa wa masu Æ™anana da matsakaitan sana’o’i da kuma shirin ciyar da ‘yan makarantun furamare.
Shugaba Tinubu ya amince da kafa kwamitin shugaban ƙasar na musamman, ƙarƙashin jagorancin ministan kudi da tattalin arziki, Wale Edun, don gudanar da bincike kan yadda ake tafiyar da shirye-shiryen rage raɗaɗin talaucin a ƙasar.
Shugaban Æ™asar ya kuma É—ora wa kwamitin alhakin gaggauta gudanar da cikakken nazari da binciken kuÉ—i da tsare-tsare da Æ™a’idojin shirye-shiryen domin sake musu fasali ta yadda za a inganta su ta hanyar kawo cikakken tsari a tafiyar da shirye-shiryen domin sake inganta su.
Mambobin kwamitin sun haÉ—ar da Ministan kuÉ—i da tattalin arziki a matsayin shugaba.
Sai ministocin lafiya da walwalar jama’a, da na kasafin kuÉ—i da tsare-tsare da na yaÉ—a labarai da na sadarwa da kuma Æ™aramin ministan matasa a matsayin mambobi.
Shugaba Tinubu ya ce kwamitin na musamman zai yi aiki don maido da martaba da kimar da shirye-shiryen suka rasa a zukatan ‘yan Æ™asar.
Ya kuma ce kwamitin zai tabbatar da inganta shirye-shiryen ta yadda za su riƙa isa wajen masu ƙaramin ƙarfi a ƙasar waɗanda dama domin su ne aka ƙirƙiro da shirye-shiryen.
Copy daga BBCHausa