BBC Hausa kafar yaɗa labarai a harshen Hausa ce, mallakin tashar labarai ta BBC da turanci wato (British Broadcasting Corporation (BBC) World Service wadda take watsa shirye-shiryen ta a harshen Hausa musamman ma labarun da suka shafi ƙasashen Nigeria, Ghana, Niger da kuma sauran masu jin harshen Hausa dake a yankunan Yammacin Afrika. Bangarene na harsunan da BBC ke watsa shiryeshiryen ta guda 33 wadanda guda 5 daga cikin su yarukan Afrika ne. Ana watsa shirye shiryen sashen na Hausa kai tsaye daga babbar tashar ta BBC dake birni Landan wato Broadcasting House da kuma tashar ta dake babban birnin taraiyar Najeriya Abuja dakuma shafinta na yanar gizo wanda ake wallafawa duka dai a birnin na Abuja.
Shafin yanar gizon BBC Hausa: https://www.bbc.com/hausa
A game da BBC Hausa: https://www.bbc.com/hausa/game-da-mu-37377088
Domin tuntubar BBC Hausa: https://www.bbc.co.uk/hausa/send/u50853335
Source: https://www.bbc.com/hausa & https://ha.m.wikipedia.org/wiki/BBC_Hausa