MU KYAUTATA RAYUWARMU – Haskenews-All About Arewa

kazama mai kula. Ba ko wana abune zaka roka kuma ka sameshi nan takeba. Kaidai tsaya kaji hikima ta ubangiji. Shidai Allah mai tsananin kunyane, kuma yanajin kunyar bawansa yayin da ya cire hannuwa zuwa gareshi, ace be samu biyan bukatarsa ba. Hikimar ubangijin tanada yawa sosai, duk sanda ka cire hannuwanka ka roki Allah akan wata bukata, to dayan abubuwa hudu ne zasu afku. Kodai ka samu biyan bukatarka kamar yadda ka roka, ko ka samu fiyeda haka, ko kuma watakil Ubangi acikin iliminsa ya riga ya sanya cewa wanan abun bazai zama Alkhairi agareka ba don haka seya canza maka abinda ka roka din amaimakonsa seya baka abinda yafi shu albarka. Ko kuma ubangiji ya dauki ladan wanan addu ar ya kankare maka zunubanka, ko kuma ya amfanar dakai ta hanyar kiyayeka daga wani sharrin anan duniya ko a lahira. Ko kuma ubangiji ya daukaka darajarka a lahira saboda albarkacin wanan addu a.                     Don haka kadena bakin ciki don bakaga biyan bukatarka da gaggawa ba, lallai Allah yana sonka kuma yana sane dakai. Kaidai kyautata zatonka gareshi ka huta da zuciyarka, wanan shine.

Kuma ubangiji yana sane bai manta dakai ba. Tunani mai zurfi da nazari shine ma aunin dake sanya mutum ya gane cewa  komai da lokacinsa, idan yau ranace to gabe ma ranace, kuma yauda gobe se Allah, zakaran da Allah ya nufa da cara babu makawa se yayi, kada ka tsanatanwa kanka kan abinda baka da iko akai, Allah shikeda lokacin zartar da abinda yai nufin faruwar sa, domin yana sane dakai,  bai manta dakai ba, tabbas lokaci zamani ke nuna kai wane, idan Allah ua tashi daukaka bawan Sa babu Wanda ya isa ya hana, alokacin ne zaka fahimta lallai komai lokaci yake jira. Mataki na rayuwa yakan gudana ta yadda Allah ya kaddara faruwar sa, matukar idan rabo ya rantse hakika babu abinda ze hana faruwar abinda tuncan rubuce yake wajen mahaliccin kowa da komai, koda bai faru yauba lokaci yana nan tafe da yadda Allah ze faru, hakan yake kan kowa. Babban makami shine,  sakan kancewa Kayi yakini, da al amarin Ubangiji, domin shi yasan yadda ya tsara, kuma shi yasan yadda abinda ze kasance cikin ikon sa, da kuma yadda Sa, dukkan jinkiri cikinsa da Alkhairi, matukar anyi hakuri za aga ribar haka, ko shakka babu. Komai da lokacin sa, Kayi fatan faruwar abu mai kyau tattare dakai, sanan ka zama mai kyautatawa Allah zato baze taba tauye maka komai. Kada ka cigaba da tada hankalin ka, mezesa ka dunga  damun kanka, bayan kasan Allah yana sane da duk abinda yake damun ka, kuma yafi kowa sanin damuwarka ko wata irice,  ka kwantar da hankalin ka, yanayi na rayuwa ba yadda baya kasan cewa kabarwa Allah komai.

Check Also:  YADDA ZAKI ZAUNA DA KISHIYA

www.haskenews.com.ng

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *