Wasu Kalmomin Hausa Da Ma’anarsu A Turance – Some Hausa Words And Their Meaning In English

By Umar Ibrahim Sade.

Yafiya = Forgiveness

Tausayi = Pity

Tausayawa =Sympathy

Tausasawa = Compassion

Sassauci =Leniency

Rangwame = Clemency

Rahama =Mercy

Kau da kai = Overlooking

Juyayi =Empathy

Jajantawa = Condolence

Haƙuri =Patience

Alhini = Mourning

Alfarma =Favor

Afuwa =Pardon

Acceptance = Karɓuwa

Zaman lafiya = Peace

Yarjejeniya = Treaty

Sasantawa = Conciliation

Manta baya = Magnanimity

Lumana = Peacefulness

Lafawa = Pacification

Kwanciyar hankali = Tranquility

Juriya = Forbearance

Ijma’i = Consensus

Haƙuri da juna = Tolerance

Fahimtar juna = Understanding

Alƙawari = Pact

Ta’addanci = Terrorism

Samame = Incursion

Rashin-tausayi = Brutality

Rashin imani = Ruthlessness

Mamaya = Invasion

Hari = Raid

Harbi = Firing

Gaba = Hostility

Fir’aunanci = Savagery

Fatattaka = Chase

Farmaki = Attack/Assault

Dirar-mikiya = Blitz

Bara = Charge

Azabtarwa = Cruelty

Artabu = Combat

Batakashi = Shoot-out

Ɓarin-wuta = Shelling

Faɗa = Fight

Fitina = Skirmish

Gumurzu = Dogfight

Jahadi = Crusade

Karon-batta = Clash

Rikici = Conflict

Taho-mu-gama = Ram

Tarzoma = Riot

Tashin-hankali = Violence

Tawaye = Rebellion

Yaƙi = War

Zubar da jini = Bloodshed

Gaba-da-gaba = Confrontation

Kai-hannu = Exchange blows

Kai-ruwa-rana = Tussle

Karo = Encounter

Kokuwa = Duel

Rigima = Dispute

Rikitarwa = Controversy

Ta-da-jijiyar-wuya = Altercation

Ta-da-ƙayar-baya – Intimidation

Taƙaddama =Contention

Tashin-tashina = Brawl

Tirjiya =Resistance

Cacar-baki = Shouting match/Exchange words

Gardama = Scuffle

Hatsaniya = Quarrel/Row

Hayaniya = Squabble

Kyara = Bullying

Musu = Argument

Sa-in-sa = Altercation

Tsangwama = Oppression

Rabuwar-kai = Fray

Ƙyamata = Resentment

Zaman-doya-da-manja = Rancor

Jayayya = Tug-of-war

Anger = Fushi

Animosity = Ƙullaliya

Antagonism = Rashin jituwa

Bitterness = Ɗacin-rai

Disagreement = Rashin daidaito

Discord =Saɓani

Distrust = Rashin yarda

Enmity = Ƙiyayya

Envy =Kishi

Grievance =Damuwa

Grudge = Riƙo

Hate = Tsana

Malice = Hassada

Misunderstanding =Rashin fahimta

Adulthood = Manyanta

Babyhood = Jarirantaka

Boyhood = Yarinta

Brotherhood = ‘Yan-uwantaka

Childhood = Yarinta

Eldership = Dattijantaka

Friendship = Abota/Ƙawance

Girlhood = Yarinta

Manhood =  Mazantaka

Oldage = Tsufa

Sisterhood = ‘Yan-uwantaka

Womanhood = Matanta

Youth = Ƙuruciya

Bakace = Sifting

Ɓarza = Crushing

Daddage = Mashing

Daka = Pounding

Dandaƙe = Crunching

Kwankwatse = Crushing

Check Also:  Shawara ga Yammata Zamani - Haskenews-All About Arewa

Marmasawa = Crumbling

Niƙa = Milling/Grinding

Shiƙa = Winnowing

Surfe = Chaffing

Sussuka = Threshing

Tankaɗe = Sieving

Tata = Filtering

Tsinta = Picking

Bakace = Sifting

Ɓarza = Crushing

Daddage = Mashing

Daka = Pounding

Dandaƙe = Crunching

Kwankwatse = Crushing

Marmasawa = Crumbling

Niƙa = Milling/Grinding

Shiƙa = Winnowing

Surfe = Chaffing

Sussuka = Threshing

Tankaɗe = Sieving

Tata = Filtering

Tsinta = Picking

Anatomy = Yanayin gaɓɓan jikin

Antibacterial = Yaƙar ƙwayar bacteria

Antibiotics = Maganin kashe ƙwayoyin cuta

Arthritis = Amosalin gaɓɓai

Gynecology = Ilimin mahaifa

Histocompatibility = Dacen-jin

Laxative =Kasayau

Mortality = Yiwuwar mutuwa

Physiology =Yanayin jiki

Tumor = Ƙari

Sputum = Kaki

Sneezing = Atishawa

Pain = Zogi/Raɗaɗi

Nasal swab = Kwarfatar hanci

Nasal Congestion = Cushewar hanci

Mucus = Majina/Gamsai

Infect = Harba

Flu = Mura

Fever = Masassara/Zazzaɓi

Cell = Tantanin halitta

Bronchitis = Mashaƙo

Addiction = (Zamewa) Jaraba

Acute = Mai muni

Available = Mai samuwa

Liable = Ɗaukar alhaki

Memorable = Abin tunawa

Noticeable = Mai ban-mamaki

Objectionable = Abin ƙi

Permissible = Halattacce

Pliable = Mai tanƙwasuwa

Portable = Mai ɗaukuwa

Possible = Mai yiwuwa

Reliable = Tsayayye

Visible = Mai ganuwa

Vulnerable = Mai rauni

#MAGNITUDE

Faɗi = Breadth/Width

Girma = Size

Gwargwado = Ratio

Iyaka = Limit

Ƙarƙari = Reach

Kauri = Thickness

Kima = Rate

Kini = Equal

Maƙura = Extreme

Mataki = Extent

Matsayi = Stage

Matuƙa = Maximum

Nauyi = Weight

Siranta = Thinness

Tamka = Parallel

Tsayi= Height

Zurfi = Depth 

Antivirus = Manhajar kare cutukan kwamfuta

Antivaxer = Mai adawa da rigakafi

Antiseptic = Kare ɗaukar cutuka

Antidote = Makari

Anticrime = Yaƙar manyan laifuka

Antichrist = Magabcin Kristi

Anti-venom = Kardafi

Anti-party = Zagon ƙasa ga jam’iyya

Anticorruption = Yaƙar almundahana

Consequently = Sakamakon haka

Daily = Duk rana

Explicitly = A sarari, Ƙuru-ƙuru

Formally = Bisa ƙa’ida, A hukumance

Fortunately = Abun birgewa

Happily = Abin farin ciki

Only = Kacal, Kaɗai, Kawai

Publicly = A bainar jama’a, A fili

Sufficiently = A wadace

Timely = A kan lokaci

Agara = Achilles tendon

Allon kafaɗa = Shoulder blade

Check Also:  Me yadace Kiyi Kafin/Lokacin Aure

Damtse = Upper arm

Dunduniya = Sole

Haƙarƙari = Rib

Hammata = Armpit

Ijiya = Eye

Karan hanci = Nose bridge

Kunci = Cheek

Kwankwaso = Pelvis

Kwiɓi = Body side

Ƙugu = Hip

Muƙamuƙi = Jaw

Sha-raɓa = Calf

Tsintsiyar-hannu = Arm

Centre for Disease Control =Hukumar Daƙile Cutuka

Coronavirus = Ƙwayar cutar numfashi

Cough =Tari

#COVID19 = Murar mashaƙo

Social distancing = Ƙauracewa junai

From 

Umar Ibrahim Sade

www.haskenews.com.ng

Leave a Comment