Mu Kyautata Rayuwarmu. Halaye da Dabi un da mace budurwa ya kamata ta tasiffantu dasu. Abu na farko dai shine riko da addininki sosai sauda kafa, babu kasala ibadarki kiriketa GAM, da zarar kinji ana kiran sallah azaharne ko la asar ko magriba ko isha ko asuba, to duk wani Abu da kikeyi a rayuwarki ki jingine shi gurin daya, kije kiyi sallahr ki akan lokaci, domin haka Allah yace kuma haka Allah yake so ayi masa ibadar sa alokacin da yace bawai a lokacin da zuciyarki take soba, matukar kina da tsarki, ma ana bakya cikin jinin al ada, yawaita yin azumin nafila kaamr na litinin da alhamis, ko kuma azumin da ake gudanarwa idan watan musulunci ya kama, azumin tasu a da ashura, ko sitta shawal guda shida da dai sauran azumun muka na nafila, to dukkan wata mace budurwa idan ta rikesu zata zama mace ta gari, insha Allah, indai kina yinsu tsakani da Allah, domin samun awajen Ubangiji, to insha Allah zaki kasance cikin kariyar Allah, amma idan kinayi ne don mutane su gani suce kinyi to gaskiya ba lada sedai tarin dunbin zunubi. Riko da iyayenki sauda kafa biyayya garesu, idan sunce wance bari sau daya tak, to kada ki yadda ki kara aikata abu harsu kara miki magana ta biyu, idan sunce kiyi Abu atake ki tashi kiyi abinda suka umarceki da yinsa alokacin da suke so, ba tareda sun kara miki magana akaro na biyu ba, kiyi musu shi alokacin da suke so, bawai alokacin da zuciyarki take soba, matukar wanan abun ba sabon Allah bane
Related Posts
Illolin Da Zina Take Haifarwa Acikin Al’ummah
- Admin
- March 10, 2023
- 0
Zina wata babbar musifa ce da bala’i da da dukkan sharri, da take ruguza al’umma taeke wargaza iyali take tarwatsa gari, take rushe mutunci da […]
SIFFOFIN WANDA AKE SO A AURA.
- Admin
- November 9, 2023
- 0
SIFFOFIN WANDA AKE SO A AURA. Akwai siffofi da ake so, miji da mata su kasance sun siffantu da su, tun kafin sunemi junansu da […]
YADDA ZAKI ZAUNA DA KISHIYA
- Admin
- December 9, 2023
- 0
YADDA ZAKI ZAUNA DA KISHIYA. Kishiya mai tsafta shine, kishiya ta rinka rige- rige da kishiyarta wajan kyautatawa mijinsu, matsalar anan shine menene yake kawo […]