Labarin da Munka Samu Daga Majiya Mai Tushe Akan Tsarin Npower Dangane da Biyan Kudaden Masu Biyar Bashi
Halin Yanzu Rukunin C1 Kimanin Akwai Wadanda Basu Samu Biyan Watannin September. October. November ba, Za’a Biyasu Sauran Kudadensu Bayan An Gama Biyan C2 Gaba Daya.
Don Haka da Wanda Yake Shortlisted da Wanda Yake Pre-selected da Applicant Duka Zasu Samu Kudinsu Matukar Sun Cika Ka’idodin Daya Dace
Hukumar Npower Zata Biya Ma’aikatanta Na C2 Babu Zato Babu tsammani a Kowane irin Lokaci, Cikin Dare ko Rana Duka Biyan Zai iya Kasancewa
A Kokarin Dr. Betta Edu Na Ganin Takawo Sauyi Akan Wannan Al’amarin Shiyasa Takeson Nuna Hazakarta Wajan Biyan Mutane Hakkinsu
Don Haka Muna Taya Duk Wani Ma’aikacin Npower Wanda Ya Cika Ka’idodin Cancanta Murna Samun Albashinsa Daga Yanzu Har Zuwa Kowane irin Lokaci.
Marubuci: Abdulrahman da Abba A Dange