labarin hatsari da ya faru a tekun Atlantika(Titanic)

Ana ta yamaɗiɗi da labarin wani hatsari da ya faru a tekun Atlantika can gaɓar yammacin duniya. Amma turancin ya yi yawa kuma bayanai mabanbanta suna ta karakaina ta yadda mutanen mu ya kamata su fahimci menene ya faru. Shine dalilin da yasa na tsakuro muku waɗannan bayanan. Wannan zai taimaka suma mutanen mu, su tofa albarkacin bakin su, bugu da ƙari kuma su yi taba ka lashe da ɗumbin darussan da suke cikin wannan tsautsayin da ya afkawa wa waɗannan ƴan talikai. 

A zamanin Sarkin Kano Muhammadu Abbas, aka ƙera wani ƙasurgumin jirgin ruwa mai suna RMS Titanic a ƙasar Birtaniya da ya tashi daga garin Southampton a ranar Laraba,10 ga watan Afrilu na shekarar 1912 da niyyar zuwa birnin New York ta Ƙasar Amurka. Wannan danƙareren jirgi wanda duniya bata taɓa ganin kamarsa ba a wannan zamani(ƙwarai ma kuwa), yana maƙare ne da fasinjoji 2,224. 

Cikin talatainin dare, kwana 4 da tashin jirgin daga tasha, ya dunguri wani ɗirkeken shuri na daskararriyar ƙanƙara. Awa 2 da minti 40 da faruwar wannan azal, sai jirgin ya yi alkafura zuwa ƙasan teku. Alƙaluman masana sun bambanta amma mafi wanzuwar su shine fasinja sama da 1500 suka salwanta babu su babu labarin su!

Binciken masana ya nuna cewa jirgin ya nutse nisan da ya kai kusan kilomita 3 da ɗigo takwas. Bari inyi maka gwari-gwari: ya kai nisan daga Ƙofar Na’isa zuwa tsohuwar jami’ar Bayero! Tabɗijan! Kaga kuwa ko kaine talibanban ko kada wajen iya ruwa, idan ka faɗa irin wannan zurfin fa, toh sai dai ƙudura ta Rabbani!

Check Also:  Shawara ga Yammata Zamani - Haskenews-All About Arewa

To wannan labarin da ya gama duniya fa a kwanakin nan, ana magane ne akan wasu mutane 5, yan ƙasa jannati, masu yawon gani da ido domin kuwa ba buɗe ido suka je ba. An ƙera musu ɗan ƙaramin jirgi da bai kai girman motar roka ta ɗaukan itace ba wanda suka biya kuɗin fasinja na kwatankwacin miliyan 185. Babu ataciman kuma. Sunje ne su ga mushen wancan shahararren jirgin ruwa da ya yi tuntuɓe shekaru 111 da suka wuce. A yadda aka tsara, jirgin nasu da ya nutsa ranar Lahadi da ta gabata da ƙarfe 7 na safe, ya kamata ya yi alkafura zuwa dandarin teku inda Titanic ɗin yake a cikin awa 2, amma ƙarar kwana tasa aka daina jin ɗuriyar sa bayan awa 1 da minti 45.  Jiya Alhamis aka fasa labarin ganin diddigar ɗan ƙaramin jirgin waɗannan mutane. Amma fa su ɗin sanin gaibu sai Allah.

Bari ka sha wani bayani akan waɗannan fasinjoji guda 5. Shifa goga kasan hanya, matashin dattijo, Stockton Rush, mai shekaru 61, shugaban tafiyar tasu, ya jima yana wannan harkar kuma gogaggen mai ji da kansa ne kamar wanda ya sha tabara yasha yasin a harkar ninƙaya. Na biyunsu kuma, Hamish Harding, hamshaƙin attajirin Birtaniya, ɗan shekara 58 ba baƙo bane wajen kasada. Da kakar bara ma, da shi aka je wata tafiyar kasada da ƴan sama jannati suka zungoro maganiɗison sararin Subuhana na ƴan mintuna wanda attajirin nan na Amurka Jeff Bezos ya jagoranta. Na ukun su, wanda shi ya kwana biyu ma, Paul-Henri Nargeolet, ɗan shekara 77, sau 35 yana alkafura zuwa wannan wurin da suka ɓata! Shi wannan dattijon fa sarkin ruwa ne, kuma ko Mai Kilago ya kamata ace yana shayin sa! Tun shekarar 1987, ya fara allanbaku zuwa wurin da aka fara gano ɓurɓushin jirgin na Titanic.

Check Also:  Zaman Aure a Yau - Haskenews-All About Arewa

Mutum na 4,Shahzada Dawood, ƙazamin attajiri ne, ɗan asalin Ƙasar Pakistan amma mai lasisin zama a Birtaniya, mai shekaru 48 da ɗan sa, na cikon biyar ɗin, mai suna Sulaimanu, ɗan shekaru 19. Wani abin tausayi, shi wannan matashi, an bada labarin cewa, ƙirjin sa na ta dakan uku uku kafin tafiyar. Rabon dai ƙasar sa acan take da kuma ƙarar kwana. Allah ya ji ƙansu yasa bakin wahalar kenan.

Akwai ƙura sosai kuma za’a murza gashin baki saboda wannan haɗari domin kuwa kamfanin  OceanGate da ya ɗauki gabarar yin wannan kasada, zai amsa tambayoyi masu zafi a gaban kuliya ta ƙasar Amurka wadda wannan ibtila’i ya faru a lardin da yake hurumin ta ne. Yana da wuya iyalan waɗannan ƴan ƙasa jannati su ɗaga ƙafa. A yanzu haka ana ta guna gunin cewa fa shi direban na su, kamar da kayan jari bola ya haɗa wasu ɓangarori na wannan jirgi da ya yi ɓatan dabo. Kuma rahotanni sun nuna cewa an ja masa kunne kafin tafiyar amma ƙarar kwana tasa ya yi kunnen ƙashi.

Allah Ya kyauta, Ya rabamu da aikin warhaka. Ka kiyayi Allah Malam.

Shamsuddeen Sani

www.haskenews.com.ng

Leave a Comment