Za’a Fara Tura Sakon Gayyata a 23 Ga Disamba, 2023: Labari Mai Dadi Daga Hukumar Daukar Ma’aikata Ta ‘yan Sanda Ga Wadan Da Suka Cike Aikin Yan Sanda

Hukumar daukar ma’aikata ta ‘yan sanda ta amince da fara tantance wadanda suka yi nasarar daukar aiki a rundunar ‘yan sandan Najeriya a ranar 8 ga Janairu, 2024.

Hukumar ta gana ne a ranar Alhamis a hedikwatar hukumar ‘yan sanda da ke Jabi, Abuja inda ta dauki matakai da dama dangane da mataki na gaba na aikin daukar ma’aikata.

Kakakin hukumar ta PSC, Ikechukwu Ani ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.

Ya kara da cewa, a lokacin da aka rufe tashar daukar ma’aikata a watan Disamba, an gano matasan Najeriya 416,270 da suka cika sharuddan farko na matakin na gaba, inda ya kara da cewa wadanda suka yi nasara sun hada da 315,065 na aikin gama-gari da 101,205 na kwararrun jami’an tsaro.

Ya kara da cewa, bayan rufe tashar daukar ma’aikata, jihar Kaduna, da mutane 31,117 da suka yi nasara, ita ce ke kan gaba, sai Adamawa da 29,848 da suka yi nasara.

Ani ya ce, “Jihar Anambra mai mutane 1,141 ce ke da karancin samun nasara a fadin kasar, sai Ebonyi, 1,537; Legas, 1,775 da Abia, 2,110.

“Hukumar ta bukaci ‘yan takara su gudanar da ayyukansu kamar yadda ake bukata ga matasan Najeriya masu sha’awar yin aiki a rundunar ‘yan sandan Najeriya, cibiyar da ke karkashin dokoki da ka’idoji masu tsauri, wacce kuma ke rike da horo a matsayin wani tushe na wanzuwarta.”

Ya ce ana sa ran wadanda suka yi nasara za su karbi wasikun gayyata a ranar 23 ga Disamba, 2023, don mataki na gaba na atisayen, wanda zai hada da tantancewa ta jiki da kuma tantancewa da za a gudanar a jihar ta asali.

www.haskenews.com.ng

Leave a Comment