YADDA ZAKI ZAUNA DA KISHIYA

YADDA ZAKI ZAUNA DA KISHIYA.

 Kishiya mai tsafta shine, kishiya ta rinka rige- rige da kishiyarta wajan kyautatawa mijinsu, matsalar anan shine menene yake kawo matsalalo tsakanin kishiya da kishiya, za a iya bin hanyoyi da za a  magance matsalar, ta yadda zaki zauna da kishiyarki lafiya, be kamata mata suna kasa  fahimta idan aka kara aure, ko kuma sun fahimta amma sesu jahilci abin da wata manufa Mara kyau, mene aciki idan aka kara miki aure, Nasani akwai kishi, amma  irin na hankali da nutsuwa, da sanin ya kamata, ba irin Wanan kishin na zamani Mara kangado da lissafi, yayin da aka kawo was uwar gida abokiyar zama, wasu sukan tarbar amaryar da mummunan zaton cewa zata rainata, haka itama amaryar takanyi mummunan zaton cewa bazasu zauna lafiya da uwargida ba, Wanan ne kesa da zarar sun hadu ba wuya suyi rigima, amma inda ace kowace acikinku, zata tarbi yar uwarta da kyakyawan zaton, har taga kamun ludiyanta, to da baza a samu matsala ba. Saboda haka idan kece uwargida kin raina kanki, to kisani cewa tamkar kin bullowa da amaryarki  salon koya mata salon zama na mugunta, ne ki kwana da sanin Wanan, duk kibi ki daga hankalinki ki nuna wa Mijin da ita  kishinki afili, bayan kin manta  yace ai, daga daya har zuwa hudu, To alokacinne amarya takeyin training awajanki har zuciyarta tazo ta bushe ta gane cewa itama zata iya miki komai idan  kin nemata, daga nan se kema kiji azuciyarki da ita da Mijin zaki iya musu komai idan kishinki ya motsa, daga nan kuma se shedan ya samu waje se  zuciyarki ta fara raya miki abubuwa marasa kyau da sake sake na mugunta ko kulla makirci ko sihirce sihirce, Wanda duk wadannan bazasu kaiki ga hanya mai bullewa, maimakon wannan yar uwa, gwara ki tsaya ki nutsu ki dubi alkibla, kiyi addu a Allah yabaku zaman lafiya kuma ki zauna da ita zuciya daya ba mugunta, ba kyashi, ba hassad,  se ubangiji ya dubeki, Wanan itace shawara mafi dacewa idan kikabi da zaki zauna da kishiyarki lafiya.

Check Also:  MATSALAR MATAN MU A YAU JINNIL ASHIQ

www.haskenews.com.ng

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *