YADDA ZAKI MALLAKE MIJINKI ASAUKAKE

 Akan mallake maza asaukake, ba tareda shan wahalaba amma         se kin zama daya daga cikin irin wadannan mata,       ki zamo mace mai hikima da azanci wacca ta karanci Mijinta dakyau, kuma take kaucewa dukkan abinda ze haddasa matsala atsaninsu. Ki zamo mace mai taushin hali da nutsuwa wacca miji yakejin nutsuwa idan Yana tare da ita. Ki zamo mace wacca kudi bai dametaba itadai kawai mijinta takeso koda akwai ko babu. Ki zamo  mace mai hakuri da juriya babu gunaguni babu mita, da kai kara ga iyaye ko kawaye. Ki zamo macen data dauki kanta likitan mijinta idan baida lafiya domin ta bashi kulawa ta musamman da riritawa. Ki zamo mace mai saurin gane ishara mai  gane shuru da magana da motsi, da yanayin shigowa da futa. Ki zamo mai fahimtar samu da rashi da kuma yanayin dake shiga aduniya ko agari. Ki zamo akoda yaushe mijinki ya kalleki se yaji dadi aranshi kuma yai farin ciki. Ki zamo maijin maganar mijinki yi nayi, bari na bari. Ki zamo mai daukar fada da nasiha idan mijinki yai miki ba yaita nanatawa ba. Tabbas zaki zama shalale agurin mijinki idan kika rike Wanan, abubuwa da aka lissafo.

www.haskenews.com.ng

Check Also:  Yadda Zakuyi Blue Verified tick na Facebook Account Naku

Leave a Comment