Tallafin 3MTT: Yanda Zaku Yi Verification Na Nitda 3MTT Din Ku Cikin Sauki

Da farko dai inhar kasan ka cika NITDA to ka dinga duba Email dinka saboda ganin sako, wani lokaci idan kayi registration message yana zuwa instantly wani lokaci kuma sai ya dauki lokaci kafin yazo

Idan sun maka Message na biyu wanda za’a fara daukan mutum 30,000 set din farko wanda za’a fara koya musu 

A jikin message din za kaga Link kamar haka; https://b.link/3MTTregister la shiga cikin Link din zasu nuna maka ka saka Email dinka, bayan ka saka zasu maka kanada damar chanza course din da kake so koya. Idan zaka chanja sai ka chanja, idan ba zaka chanja ba sai ka barshi a inda yake

Bayan ka gama wannan, zasu nuna maka cewa ka saka Password saika saka Password din da kaga dama ka confirming din shi, daka nan kuma zasu tura maka OTP ta Email sai kayi minimize kaje kayi copying din OTP din sai ka dawo ka pasting musu a wajen da suka umarce ka

Zasu nuna maka cewa ka selecting categories guda biyu, akwai 

1- Fellow, sannan na biyu akwai 2- Training provider sai ka zabe fellow saboda fellow suna wanda za’a koya musu, su kuma Training provider suna wanda zasu koya muku training din

Daka karshe sai wajen da zasu baka Test kayi, bayan nan sai Questionnaire da zasu baka ka amsa questions 13 a cikin minti 10. Wannan shine final stage, inhar kasan baka yi daya daka cikin wannan abinda na fada ba to Verification dinka is incomplete 

Wanda kuma basu ga Message suyi hakuri sunan su zai futo a batch B bayan wanda aka shortlisting sun gama training din su na tsahon watanni uku. Allah ya bamu nasara, Allah yasa mu amfana da alkhairin dake ciki

Check Also:  An Bude Shafin Daukar Sojojin Kasa

www.haskenews.com.ng

Leave a Comment