Shugaban Hukumar kidaya jama’a ta kasa zai yiwa Tinubu bayani kan kidayar jama’a a wannan makon – Jaridar PUNCH ta wallafa

Shugaban Hukumar kidaya jama’a ta kasa zai yiwa Tinubu bayani kan kidayar jama’a a wannan makon – Jaridar PUNCH ta wallafa

Shugaban hukumar kula da yawan jama’a ta kasa, Nasir Isa-Kwarra zai gana da shugaba Bola Tinubu a wannan makon, kamar yadda jaridar PUNCH ta wallafa.

taron ba zai rasa nasaba da sabbin bayanai na gudanar da kidayar jama’a da gidaje na shekarar 2023 ba

wanda tun farko aka shirya yi a ranakun 3-7 ga watan Mayu amma an dage saboda da wasu dalilai.

Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da dage aikin zuwa wani lokaci da gwamnatin Tinubu mai zata yanke shawara.

kakakin hukumar kidaya jama’a ta kasa( NPC) Isiaka Yahaya.

 Yace “Shugaban zai gana da shugaban kasa a wannan makon amma ba zan iya ba ku takamaiman ranar ba. Muna aikin gabatar da shirin ne domin yiwa Shugaba Tinubu bayanin halin da ake ciki na shirye-shiryen kidayar.”

Hukumar kidaya jama’a ta kasa tana cigaba da tantace adadin waɗanda Zasu yi aikin Wucin gadi na kidayar jama’a biyo bayan yawan kiraye kiraye da kungiyoyi sukemata.

Hukumar tana gab da sanya Ranar ƙidaya jama’a ta kasa wanda nan da kankanin lokaci hukumar zata sanar a hukumance.

ALLAH Yasa Mu Dace Baki Daya

www.haskenews.com.ng

Check Also:  Mene ne Gaskiyar Wannan Labarin Na Aikin Kidaya ta Kasa NPC

Leave a Comment