Karin Bayani Akan Daukar Ma’aikata a Hukumar NDLEA

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta fitar da jerin sunayen wadanda suka yi Nasara.

Femi Babafemi, Daraktan yada labarai da bayar da shawarwari na NDLEA ne ya sanar da hakan ta wata sanarwa a hukumance.

Hukumar NDLEA ta gayyaci ‘yan takarar da suka yi nasarar cin jarabawar tantancewar da aka yi kwanan nan don shiga Mata kin Gaba.

Wannan muhimmin bayani ya fito ne a cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai da bayar da shawarwari na hukumar Femi Babafemi ya fitar.

Ana buƙatar ’yan takarar da aka zaɓa dasu bayyana don tantancewa  daga ranar Litinin 5 ga Yuni zuwa Juma’a, 16 ga Yuni, 2023.

An tsara takamaiman ranaku da lokutan da karfe 8 na safe kowace rana.

An yi kira ga ’yan takara da su kiyaye wa’adin da aka ware domin tabbatar da tsari mai kyau.

Anware  cibiyoyi biyar a duk faɗin ƙasar don tantancewa

Wadannan cibiyoyin sune

 Abuja   Legas

Jos Plateau  Kano

Fatakwal

Ana sa ran ‘yan takarar za su halarci gurin a rukunin da sunayensu ya bayyana a shafin hukumar ta NDLEA.

Dole ne ‘yan takara su kawo takaddun da suka dace zuwa gurin tantance wa.

Takardun da ake buƙata sun haɗa da Original da kwafin takardun 

www.haskenews.com.ng

Related

Stay on op - Ge the daily news in your inbox