October 8, 2024

Bazan taba cikaba seda kai huby, kamar yadda se an ambaci A kafin ace B to haka kaima dole Kaine gaba jagaba Kaine sarkina hukuncin daka yanke ya zartu,bazan dena kadaici ba se sanda ka daukeni ka kaini gidanka amatsayin matarka.Jigon rayuwa soyaiya ce, ni nasamu nawa jigon abokin rayuwa,taya zan iya rayuwa bakai bana iya bacci idan ban ganka ba, bana iya sukuni idan banjika, haka idan  duniya taimin zafi to rashinkane,  idan na rasaka rana zata zamto min tamkar dare, munyi sabo tamkar da’ da uwa,bani da wani amini ko aboki tamkar kai, Kaine amintaccena dakai na yarda. Samunka Alkhairi ne naji arayuwata, meson rabamu dakai samsam baze moruba, damuwata takace komai nawa hakane,  kuma koda ka mutu kana nan azuciyata har abada.

Zabin raina Kaine kasani, na kagu naga wanan rana masoyina zanyi dukkan wata biyaiya agareka zanbi umarninka bazan kiba, domin nazama matarka mallakinka, soyaiya dakai akwai zaki wane zuma,na tsaya tsayin daka sekai, sunce  na fiye naci, amma na  tushe kunnuwana daga masu gulma,nidai sekai, ya Rabin raina bango majin ginata, bana zullumin cewar ka zamo uban yayana, nasan kanada Alkunya gami da tarbiya, ka  dasa kaunarka azuciyata, dole samari suyi hakuri koda sun kwankwansa bazasu samuba, tazama taka, Kaine rayina daidai dani, dkaine  zaka cika min mafarkina dakai zana zauna,tabbas nasan zan morewa rayuwa nazama Zara acikin taurari,nazama bar kwatancen acikin kawaye, darling,  sonka araina  tamkar zanen zabuwane baya gogewa bare ya disashe.

www.haskenews.com.ng

Check Also:  Yan Arewa mu Farka Dama ga Masu Kwalin SSCE, Diploma, Degree ko Masters: An Bude Shafin Cike "Alliance for Youth Nigeria Vocational Skills Training"
IMG_4780-768x768.jpg Screenshot_20230916-075028.jpg

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *