Kalaman Soyayya 2024/2025

Kalaman Soyayya 2024/2025

Yadda zaki tarbi saurayinki yay in da yazo zance. Alokacij da yazo gurinki zaki futo cikin nutsuwa, da hankali, cikin kamala, sanan kiyi sallama, idan ya amsa se kiyi gaisuwa bayan ya dan nutsu azaune ko a tsaye ne, sanan kice barka da zuwa kalbina da fatan kazo lafiya, ya hanya, nasan kasha wahala ahanya, to kayi hakuri lefi nane, nasa hubbyna ya gaji zakina fada acikin salo na birgewa da nutsuwa tare da nuna kulawa agareshi. Sanan kada ki kafeshi da idanunki ido cikin ido sedai ki rinka risnawa, kada ki rinka zakewa dayawa, har saurayinki ya dinga tinanin baki da kunya koda kinada ita, ki maida hankalinki yayin da yake miki zance musanman me  mahimmanci, ki nuna kina ganewa koda bakya gane zancen da yake miki,  kada alokacin kice ni bana ganewa ah, ah ba haka zakiyi ba, sedai idan ya Dan tsaya se kice, dear dan kara yimin bayani naji kaji, ina so na kara fahimta ne, kada ki rinka datsar zancen da yake idan yana magana, kina bari yana kara sawa.

Idan bkuna zance da saurayinki ki zamo mai kawo mai zatuka masu ma ana ko wadanda zasu dinga sashi farin ciki, ba shirme da hashanci ba, kada ki rinka fadar sunanshi gatsal haka ba sayawa, domin yana so ki sauyamai suna mai dadi amatsayin shi na masoyinki wanda kike burin aura nan gaba, kamar idan yau  kince mai habiby, agaba kuma sekice mai kalby ko mai Sweet heart, da dai sauransu gasunan kala kala, masu dadi zamu kawosu agaba insha Allah,

Idan ya gama zancen ze tafi kada ki bari ya tafi ba tareda kin gayamai wata kalma mai dadi, mai sanyaya rai ko mai ma ana da ze tafi yana tuna nunki tareda karuwar kaunarki aranshi, game da Addu a da fatan Alkhairi agareshi, kamar kice, Allah ya tsare minkai ya karemin kai, ubanguji ya kaika lafiya, ya ya tsareka daga dukkan sharrin makiya da abin ki, kada ka manta da addu ar yanzu idan zaka tafi, sanan kidan yi shuru, idan ya tambayeki mene, sekice wallahi banaso rabuwa dakai ban gaji da ganinka ba, babyna yaushe zaka dawo, don Allah ka dawo da wuri kaji, irin a shagwabannan sannan sekice seda safe, na barka lafiya, kaje gida ka huta. 

Bayan kun rabu, ya koma gida karkice seya kiraki ah ah, kiva kirakiba ke ki kirashi awaya kiyi mai ban gajiya, kice Yaya kaje gida masoyina, dafatan kaje gida lafiya, yayin daya amsa miki yaje lafiya, seki nuna jin dadinki kice masha Allah, naji farin cikin jin hakan sosai, na gode Allah, dama kiranka nai naji ka isa lafiya, yanzu seda safe ka huta, kada ka manta da addua, kai mafarkina kaji Honey by by

www.haskenews.com.ng

Related

Stay on op - Ge the daily news in your inbox