Kalaman Masoya – Haskenews-All About Arewa

 Kalaman Masoya

Ina son Wanda yake sonka masoyina, haka ina kin Wanda yake kinka abin kauna, Kaine Wanda kasa na zamo Zara cikin taurari, Kaine na zaba amatsayin abokin rayuwa, na baka iko akaina kai yadda kaso bazan taba yi maka goriba, dukkan ajin dake agareni babu shi yanzu na sauko   akoda yaushe ashirye nake dana shigo cikin gidanka saboda zuciyata ta aminta dakai   dari bisa dari, kuma kayi karkon da baze gusheba agareta. Tabbas zan iya mutuwa saboda kai Indai zaka rayu, bazan taba guje makaba, bazan taba baka kunyaba, ba zansa kai kukaba. Bana fargaba kuma Bana shakka Shiga dakai ko ina, zani dakai ko Ina, zan tsaya dakai ko ina, kuma zan nuna ka ako ina agaban ko waye bazanji kunya ba domin nasan ka cancanta kuma ka kai fiye da haka ma kuma nasan bazaka bani kunya ba. Babu kara ga duk wanda yace ze tabamin kai domin ashirye nake na bada rayuwata saboda kai. Banaso kaimin tazara banaso kai nisa dani inajin zafin rashinka kusa dani ina gaza jure rashinka atare dani, sauki daya danakeji yake ragemin dadadin rashinka, idan na tuna cewa  zaka zamo angona wata rana,nakanji farinciki idan na tuna kalaman ka masu dadin sauraro tare da sautin muryanka mai taushin tausasawa, koda raina abace yake nakanji sanyi yayin dana tuno rarrashinka agareni  da sani dariya lokacin danake fushi. Koda baka nan, kayi nesa da idanuna amma kana nan acikin zuciyata, jini da hanta jini da fata kashi da soka sam ba zasu rabuba haka muma bazamu rabuba, koda za a shekara dara hubby matsayinka araina bazaya  canzuba

www.haskenews.com.ng

Leave a Comment