Abubuwa da zasu hana ka cin gajiyar aikin NPC koda anyi maka Approval

Abubuwan da zasu hana mutum cin gajiyar shirin aikin kidayar jama’a koda anyi masa Approval na neman aikin kidaya da mutum yayi .

Abu na farko shine lokacin da kayi rijista baka sa Email address dinka ba tare da phone number ko Kayi kuskure wajen sakawa 

Saboda data wannan email address ne za’a gayyace ka zuwa karbar horo 

Abu na biyu shine anyi maka approval wani matsayi wanda ba Enumerator ba ko Supervisor .

Saboda acikin watan nan za’a gudanar da horo na massman ga bangarorin nan biyu ko mutum yaki halatar taron horarwa 

Abu na uku lokacin da kazo registration na neman aikin kidayar baka yi rijista complete ba ,akwai bayanin masu bukatar mahimmanci daya kamata ace ka shigar .

Amma acikin hukuncin Ubangiji ka biya kudi anyi maka approval toh hakika ba zaka samu damar cin gajiyar shirin ba saboda ka biya kudi shiyasa masu Approval Suka yi maka wanda inda lokacin da ake tantance mutane da ba zaayi maka ba saboda bakayi registration complete.

Rashin dora hoton Result dinka wato shaidar kammala Karatu ita ma zata iya hana mutum cin gajiyar shirin Koda ko ya samu Approval ,kudin daya bayar shiyasa aka yi mishi Approval.

Ku sane duk bayanin mutanan da suka nemi aikin nan da wanda suka samu Approval da ma wanda basu samu ba duk data dinsu yana abuja.

Ku cigaba da bibiya ta in Sha Allahu dade ko babu dade zan ke sanar daku wasu abubuwa masu bukatar mahimmanci game da kidayar nan In Sha Allahu.

www.haskenews.com.ng

Related

Stay on op - Ge the daily news in your inbox