kazama mai kula. Ya kai, ke, yar uwa, dari bisa dari rayuwa tafi dadi idan baka zamo mai yayata ko wana sirri nakaba ga kowa, haka kuma kafi samun nutsuwa arayuwarka yayin daka fita abinda babu ruwanka, idan zakai shawara don cimma wani buri na rayuwa, to zakai ne da wadanda sukaje inda kake son zuwa ba wadanda basu kaiba, Rayuwa ba ko yaushene take zuwan maka a yanayin da kake soba, dole ka tashi ka nema, Kada ka taba kuskuren matsawa wani dole seya shigo rayuwarka, ko kai kace seka shiga tashi rayuwar, Dole ka koyi danna fushinka, domin duk zuciyar da take iya danna fushi zata iya karbar ko wane yanayi idan yazo na rayuwa, Domin guje takaici ka dinga mu amala da kowana mutum arin yadda yazo maka, bawai yadda kakeso ka sameshiba, Duk Wanda ya nunama fuskar wayeshi, Kawai Kayi hakurin bashi lokaci, Ka kula da rayuwarka matukar gaske, samun matsarka baze hanaka ci gaba da rayuwaba, Ba ruwan kowa dakai arayuwarnan, kaidai Kawai kai aiki tukuru kaje wani mataki da za ai alfahari dakai arayuwa, Idan baka tsaya ka gina rayuwarka da kyau ba to tabbas bazaka da kyau ba.